Advertising
Advertising
Labarai

Asirin wata matar aure ya tonu bayan ta yiwa ‘yar kishiyar ta asiri ta mutu sabida tana bakin cikin za’a mata aure

Asirin wata matar aure ya tonu bayan ta yiwa 'yar kishiyar ta asiri ta mutu sabida tana bakin cikin za'a mata aute

Kamar yadda kuka sani dai har yanzu ana samin matan aure wanda suke da tsananin kishi da har yake kai su ga aikata aikin dana sani, wanda a yanzu muka sami labarin wata matar aure ta kashe ‘yar kishiyar ta sabida zata yi aure.

Advertising

Wata matar aure ce suka hada baki da kawar ta inda ta rakata wajan boka ta sanar masa da cewa, ‘yar kishiyar ta ce zata yi aure har ma an sama mata rana amma ita tana bukatar wannan aure da za’a yi ya lalace domin bata bukatar ayi auren.

Bayan matar tayiwa bokan wannan bayani sai ya tambaye ta kan cewa, mai take bukata ayiwa yarinyar wato ‘yar kishiyar ta ta sai ta fada masa cewa tana bukatar a kashe ta.

Nan take sai bokan ya dauko wata kwarya ya fara zuba ruwa a ciki tare da barbada garin magani, bayan ya gama sai ya kira sunan yarinyar nan take sai yarinyar ta bayyana a cikin kwaryar tana dariya.

Advertising

Sai bokan ya dauko allura ya fara caccakawa a cikin kwaryar da yarinyar ta bayyana nan take sai aka ga yarinyar tana ihu ta rasa inda zata saka kanta.

Nayan matar da kawarta bar wajan bokan sun koma gida sai suka tarar da ana shirye-shiryen jana’izar ‘yar kishiyar ta ta wacce za’a yi auten, amma bayan nan kawar matar ta tona asirin abin da ya faru kan abin da suka aikatawa yarinyar wacce za’a yi auren nata ta mutu.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekken bayani daga bakin wani Malamin addini, akan matar da ta kashe ‘yar kishiyar ta sabida tana bakin cikin za’a mata aure.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button