Advertising
Advertising
Labarai

Jam’iyyar APC ta samar da wani tsari na raba mukami tsakanin Gwamna Ganduje da Ibrahim Shekarau

Jam'iyyar APC ta samar da wani tsari na raba mukami tsakanin Gwamna Ganduje da Ibrahim Shekarau

Jam’iyyar APC mai mulki a yanzu ta samar da wani tsari na raba mukami tsakanin Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim.Shekarau.

Advertising

A cigaba da zaman sulhu tsakanin bangarori guda biyu da suke ta rikicin na mallakar jam’iyyar tun bayan kammala zaben shugabannin jam’iya, to a jiya Asabar ne Kwamitin riko na jam’iyyar APC ya kira jagororin biyu da suje babban birnin tarayya Abuja domin wata ganawa da za’a yi ta gaggawa, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Bayan an shiga taron gaggawar a birnin Abuja karkashin jagorancin Mai Mala Buni Gwamnan Jihar Yobe, jam’iyyar ta yanke shawarar tura wani kwamiti mai karfi zuwa jihar Kano domin tabbatar da anbi sabon tsari wanda za’a raba mukaman jam’iyyar daidai.

A wata sanarwa da aka yi bayan taron da aka gudanar a jiya Asabar da daddare mai magana da yawun Sanata Ibrahim Shekarau “Sule Ya’u Sule” ya tabbatar da cewa, jam’iyyar ta samar da tsarin sanya kowa cikin harkokin jam’iyyar ta APC a jihar Kano.

Advertising

Kamar yadda “Sule Ya’u Sule yace, ranar Litinin za,a sanar da duk bangarori biyun halin da ake ciki, kuma za’a kafa kwamiti mai karfi daga sakatariyar jam’iyyar kuma a tura shi jihar Kano don tabbatar da bin ka’ida da aiwatar da tsarin da za’a yi a ranar Litinin.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button