Uncategory

Jarumin kannywood Lawan Ahmad Umar Hashim a izzar so ya samu lambar yabo a jami’a Jigawa, Dutse.

Jarumin masana’antar kannywood Lawan Ahmad Wanda ake Kira da (Umar Hashim) acikin shirin izzar so fim mai dogon zango, yasamu lambar girmamawa a jami’ar Tarayya dake jihar Jigawa, Dutse.

Lawan Ahmad yasamu wannan lambar girmamawa sanadiyyar shirin fim Mai Farin jini na izzar so, kasancewar yadda Shirin yake koyarda abubuwa da dama musamman abinda ya shafi rikon Amana, gaskiya da kuma nuna girman addini musulunci.

Izzar so ya kasance shine shiri na farko a Fina finan Hausa Wanda yasamu lambobin yabo daga wajan kungiyoyi masu Zaman kansu Haka daga wajan malamai kasancewar yadda ake koyarda abubuwan dasuka shafi addinin musulunci acikin fim din.

Fim din yayi rawar gani wajen fadakar da mutane abinda suka manta a harkar rikon amana da nuna gaskiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button