Maharan ‘yan bindiga sun hallaka Mata da kananan yara a kauyen Zamfara lokacin da ake Sallar Juma’a
Maharan 'yan bindiga sun hallaka Mata da kananan yara a kauyen Zamfara lokacin da ake Sallar Juma'a
Subahanallahi duniya ina zaki damu muna rokon Allah ya kawo mana dauki a kasar mu Nageriya kan ta’addancin da yaki ci yaki cinyewa.
A yanzu haka mun sami labarin wasu maharan ‘yan bindiga sun hallaka mutane wanda a kalla zasu kai ashirin, kuma dukkan mutanen da suka hallaka yawanci mata ne da kananan yara a karamar hukumar Bungudu da Tsafe dake jihar Zamfara.
Wasu mutane mazauna yankin sun bayyana cewa, harin da ‘yan bindigar suka kai kauyen ‘yar katsina dake karamar hukumar Bungudu, an hallaka mutane sun kai goma, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.
Maharan ‘yan bindigar wanda yawan su zasu kai su dari sun kai harin ne a kan babura sannan suka sace wasu mutanen, a daidai lokacin da mazauna yankin ke gudanar da sallar Juma’a.
Wani mutumi wanda shaidar gani da ido ne ya shaida cewa, maharan ‘yan bindigar sun zo da yawan gaske a kan babura sannan suka bude wa mutane wuta a lokacin, ‘yan Sa kai sun taka rawar gani sosai wajen kai dauki a lokacin da abin ya auku.
Mutumin wanda ya gani da idon sa ya kara da cewa, sannan mafi yawan mutanen da maharan ‘yan bindigar suka hallaka kananan yara ne da kuma mata, amma wadanda suka kai harin suma an hallaka musu mutanen su.