Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Mawakan Kano sun fara fusata akan wata gasa da Rarara ya dauke amma ya kasa cikawa

Mawakan Kano sun fara fusata da kosawa akan wata gasa da Rarara ya dauko akan wakar zaman lafiyar Nageriya.

Advertising

Mawakan na johar Kano sun fara fuasata tare da kosawa aka wani al’kawari da ficaccan mawakin siyasa Dauda Kahuyu Rarara ya dauko, wanda kuma Allah bai bashi ikon cikawa ba wanda a halin yanzu kusan shekara daya kenan da ake wannan maganar.

Dauda Kahutu Rarara ta kawo wata babbar gasa tsakanin mawaka na kowanne fanni wato mawakan gargajiya da kuma mawakan hausa hip-hop, da kuma mawakan fina-finai na hausa akan cewa ko wane mawaki yaje ya feke basirar sa ya yi waka aka zaman lafiyar Nageriya.

Kuma a cikin gasar akwai manya-manyan frofesoshi dake jihar Kano wanda sune alkalan gasar, bugu da kari kuma dukkan nin gidajen radio suna cikin gasar a fannin abin da ya shafi tallatawa.

Advertising

A cikin gasar mawaki Rarara ya yi manyan alkawura da dama wanda zai baiwa mawakan da suka ci gasar, kuma an fada cewa har wadanda basu ci gasar ba za’a basu manyan kyaukuka da kuma kudade.

Wato a fannin mawakan gargajiya za’a zabi mutane 3 sannan a fannin mawakan hausa hip-hop za’a zabi mutane 3, hakama a cikin mawakan fina-finai suma za’a zabi mutane 3 inda za’a bada kyautar manyan motoci da baburan adaidaita sahu da kuma makudan kudade kamar tadda Rarara ya tabbatar a lokacin.

To a halin yanzu dai wannan gasa tayi kusan shekara daya kenan wato tun wancan azumin, kuma a cewar Rarara a cikin wancan lokacin za’a yi gasar a gama sa kuma gashi abin ya zama ba haka ba.

Kuma abin da ya sa mawakan suka fara kosawa shine tun bayan wancan lokacin har zuwa yanzu ba’a jin Rarara ya fito ya yi magana akan gasar ba, wanda hakan yasa wasu mawakan da suka wahala a cikin gasar suka fara magana.

Hakika mawaka da yawa sun sha wahala a cikin wannan gasa wajan rubuta wakar shiga gasa da biyan kudin studio domin buga wakar, da dai sauran fadi tashi a suka sha yi a dalilin shiga gasar.

To a yanzu dai abubakar Ibrahim wanda aka fi sani da Gfresh tare da dan uwan sa Al-Ameen wato wanda suke waka tare, sun aikawa Rarara sako akan lamarin gasar wanda Gfresh shi ne ya wakilci Al-Ameen wajen yin maganar.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji sakon da suka turawa mawaki Rarara akan wannan gasar da ya saka tun wancan shekarar har ta kawo yanzu.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button