Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Datti Assalafy yayi martani akan sabuwar Salma ta shirin Kwana Casa’in kan rashin da’ar da take nunawa

Datti Assalafy yayi martani akan sabuwar Salma ta shirin Kwana Casa'in kan rashin da'ar da take nunawa

Kamar yadda kuka sani a jaruma Salma ta cikin shirin Kwana Casa’in 90 mai dogon zango ta fita daga cikin shirin sakamakon wani al’amari data bayyana kan cewa, bazata cigaba da shirin ba sabida zata koma cigaba da karatun ta.

Advertising

To bayan fitar da Salma tayi daga cikin shirin Kwana Casa’in ba tare da bata lokaci ba aka maye gurbin ta da wata sabuwar mawakiya mai suna “Mufeeda.

Ba tare da bata lokaci ba aka fara haska shirin na Kwana Casa’in 90 sabuwar jarumar wato Mufeeda wacce ta maye gurbin Salma, amma bayan kwana kadan da fara haska shirin da ita sai ta bayyana a cikin wasu hotuna da suka janyo mata cece-kuce.

To a yau ma ficaccan marubucin nan Datti Assalafiy ya wallafa wani bayani akan Mufeeda sabuwar jarumar shirin Kwana Casa’in wacce ta maye wajan Salma, inda ya fara da cewa.

Advertising

Bayan bayyanar wannan yariya Mufeeda sabuwar Salma a cikin shirin Kwana casa’in na tashar Yehudawa Arewa 24, yarinyar tazo da wasu miyagun dabi’u na Yehudanci zalla da take yadawa a kafofin sada zumunta wanda hakan ya jawa suka a kanta hatta ga masu kallon shirin kwana casa’in.

Mabiya tashar Arewa 24 sunce yarinyar bata dace da shirin ba, kuma bata cancanta ba saboda dabi’unta ba irin na Kasar Hausa bane da wasu abubuwa makamantan haka To yanzu ake sanar dani cewa Arewa 24 sun cire wannan yarinya daga cikin shirin kwana casa’in, sun nuna tayi margaya sala a cikin shirin film din.

Allah ka amintar damu daga Arewa24.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button