Labarai

Kotu ta yankewa Sadiya Haruna hukuncin watanni 6 a gidan gyaran hali kan kalama da tayi akan Isah A Isah

Kotu ta yankewa Sadiya Haruna hukuncin watanni 6 a gidan gyaran hali kan kalama da tayi akan Isah A Isah

Yanzu-yanzu muka sami labarin cewa, wata kotun majistare dake filin jirgin sama a jihar Kano ta yankewa Sadiya Haruna hukuncin daurin watanni shida ba tare da zabin tara ba.

A lokacin da aka yi zaman kotun a yau Litinin mai shar’a Muntari Garba Dangote ya yankewa Sadiya Haruna wannan hukuncin ne, bisa kalaman batanci da tayi ga wani jarumin kannywood mai suna Isah A Isah.

Sadiya Haruna tayi wannan kalaman ne a shafin ta na sada zumunta instagram, wanda hakan bayo baya ne tun bayan wani sabani da suka samu ita da jarumin kannywood din Isah A Isah.

Wanda daga nan ta fara aika masa da wasu kalamai wanda basu dace ba a cikin wasu bidiyoyi da take wallafawa a shafin nata na instagram.

Bayan haka kuma a kwananan rigimar tasu ta sake tasowa tun bayan da wasu mutane suka yi kokarin sace ita Sadiya Haruna.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button