Labaran Kannywood

Teema Makamashi ta nuna farin cikin ta bayan kotu ta yankewa Sadiya Haruna hukuncin wata 6 a gidan yari

Teema Makamashi ta nuna farin cikin ta bayan kotu ta yankewa Sadiya Haruna hukuncin wata 6 a gidan yari

Kamar yadda kuka sani a dazu mun kawo muku labarin kotu ta yankewa Sadiya Haruna hukuncin zama a gidan gyaran hali na tsawon watanni shida, bayan wasu kalamai da ta furta akan jarumin kannywood Isah A Isah.

To a yanzu kuma mun sami wata bidiyo wanda jarumar masana’antar kannywood Teema makamashi ta wallafa a shafinta na sada zumunta instagram, inda take nuna kamar tana murna da kama Sadiya Haruna da aka yi.

A cikin bidiyon zaku gabyadda jaruma Teema Makamashi take fadin wasu maganganun da suke nuna tajin dadin wannan hukuncin da kotu ta yankewa Sadiya Haruna.

Inda har take cewa, idan kasan farkon rigima bakasan karshen na ba, ita bata fada sai an tabo ta gashi nan wata zata yi shekara shida a gidan yari.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji abin da jaruma Teema Makamashi take fada tana, wanda hakan yake nuna cewa taji dadin kama Sadiya Haruna da aka yi.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button