Labarai

Wata matashiya mai suna Fatima ta sami kyauta daga Sarki musulmai bayan ta haddace Alkur’ani mai girma cikin wata 6

Wata matashiya mai suna Fatima ta sami kyauta daga Sarki musulmai bayan ta haddace Alkur'ani mai girma cikin wata 6

A wannan makon ana yawan samin mutanen da suka maida hankali wajan haddace Alkur’ani mai girma, wanda a yanzu muka sami labarin wata matashiyar budurwa data haddace Alkur’ani mai girma cikin wata shida 6.

Mahaddaciyar Alkur’anin sunzo Nageriya ita da iyayan ta daga kasar Faransa domin haddace Alkur’ani mai girma cikin wata shida.

Matashiyar mai suna “Fatima Musa” ta sami babbar kyauta wanda mai martaba Sarkin musulmai “Sultan Sa’ad Abubakar Muhammad” ya bata.

An gudanar da bikin badakyautar ga mahaddaciyar Alkur’anin wato “Fatima Musa” kamar yadda shafin BBC Hausa suka ruwaito.

Wata yarinya ‘yar kasar Faransa ta haddace Al-Ƙur’ani mai girma a cikin watanni huɗu a birnin Zaria na Jihar Kaduna.

Yarinyar mai suna Fatima Musa wadda iyayenta suka koma Najeriya daga Faransa ta soma haddar ne a wata makaranatar Islamiyya a Zaria inda ta rinƙa haddace shafi takwas na Al-Ƙur’ani a duk rana.

A yau ne aka yi bikin saukar haddar inda daya daga cikin manyan baƙin da suka halarci saukar har da Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na III da Sarkin Zazzau Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli da Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da Sarkin Kazaure Najib Hussaini Adamu da sauran manyan sarakuna.

Hukumar makarantar ta ce wannan ne karo na farko da ta samu ɗaliba mai irin wannan hazaƙar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button