Advertising
Advertising
Uncategory

Wata sabuwa: Gwamnatin Kano Zata Baiwa Makashin Hanifa Lauya Domin Bashi Kariya

Mutumin da ake zargi da hallaka karamar yarinya Hanifa Abubakar mai shekara biyar a Kano, Abdulmalik Tanko, ya fada wa kotu cewa ba shi da lauya sannan ya bukaci gwamnatin jihar ta bashi lauya wanda zai ringa kare shi.

Advertising

“Ba mu da lauya a halin yanzu saboda ba ma iya magana da kowa, amma ina mai rokon gwamnati kano tani lauya,” cewar Abdulmalik a zaman kotun na yau Litinin.

Musa Lawal Lauyan gwamnati ya ce gwamnatin za ta ba su lauyan kamar yadda suka bukata. kaman yadda doka ta tanadar sabida laifin da ake zargin su dashi babba ne.

A halin yanzu dai kotu ta sake dage zaman zuwa 14 ga watan Fabarairun 2022 da karfe 2:00 na rana domin cigaba da Shari’ar tasu.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button