Advertising
Advertising
Labarai

Abdulmalik Tanko makashin Hanifa tare da wadanda suka yi aika-aikar sun rasa Lauyan da zai kare su a kotu

Kamar yadda kuka sani wanda ake zargi da kashe yarinyar nan ‘yar jihar Kano mai shekara 5 wato Hanifa wato Abdulmalik Tanko, ya fadawa kotu cewa bashi da lauyan da zai kare shi wanda kotun ta amince da cewa za’a sama masa lauyan da zai kare shi.

Advertising

Lauyan gwamnati mai sun Lawan yace, za’a basu Lauyan kamar yadda suka bukata inda yace dama dai haka doka ta tanadar, sabida laifin da ake zargin su da aikatawa babba ne.

Wanda a dalilin Lauyan da basu da shi a zaman da ya gabata mai shari’a Sulaiman Na Abba ya daga zaman shari’ar zuwa ranar 14 ga wannan watan da muke ciki na Fabarairun.

Wato wannan watan na shekarar 2022 inda kotun zata sake zama da karfe 20:00 na ranar in Allah ya kaimu.

Advertising

To a halin yanzu dai gwamnatin jihar Kano tace zata tsayawa Abdulmalik Tanko da sauran wanda suka aikata laifin, inda gwamnatin zata basu Lauyan da zai kare su a zaman kotu na gaba.

Kwamushina shari’a na jihar Kano Barisat Musa Abdullahi Lawal shine ya bayyana hakan jim kadan bayan zaman sauraron shari’ar wanda aka yi a jiya Litinin.

Barisata Musa Abdullahi Lawal ya yi bayani ne kamar haka, muna neman a karantawa masu laifi tuhumar su, kuma irin wannan tuhumar babba ce dole sai yana da Lauyan da zai kare shi.

Kundin tsarin mulkin Nageriya ya tilasta irin wannan tuhuma sai da Lauya wannan ne ya sanya suka bukaci Lauya daga wajan mu, to kuma mun dauki alkawarin zamu tabbatar sun sami Lauya, a cewar Barista Musa Abdullahi Lawal.

Kwamishinan shari’ar ya cigaba da cewa, mun bukaci a dage shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Fabarairun ne domin kafin lokacin zamu basu Lauya.

Barista Musa Abdullahi Lawal yace, da zarar an basu shaidar gwamnati a shirye yake ya kawo karshen shari’ar cikin hanzari.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button