Advertising
Advertising
Uncategory

Ado Gwanja ya saki matarsa maimunatu a wani kishin kishin da yake fitowa.

Wani labari da muke jin kishin kishin din sa mara dadi shine wai mawaki Ado Gwanja ya saki matar sa maimuna inda muka yi bincike wata majiya ta tabbatar mana da mawakin ya sauwakewa matar tasa kuma sakin ba daya ba ba biyu ba har saki uku mun tambayi dalilin sabanin da ya haddasa sakin da tsawon lokacin da aka yi sakin bamu samu gamsashshen bayani ba amma dai an bamu tabbacin rabuwar auren masoyan da zai bakanta ran dubban masoyan su.

Advertising

Sai dai mun yi wani nazari a shafin maimunan wanda muka ga ta cire duk wani abu da ya shafu gwanjan a shafin ta hatta sunan Mr Ado Gwanja da ta sa ta cire ta sa fashion beauty shafin kasuwancin ta munat gwanja collection ma ta maidashi munat dan’auta collection.

Baya ga wannan sanin kowa ne jarumin kan shirya kasitaccen bikin birthday ga matar tasa da yar sa duk shekara amma wannan shekarar birthday din maimunan ita kadai tayi yan hotunan ta ta wallafa a shafin ta kuma ko gwanjan bai taya ta murna a shafin shi ko sashen tsokacin ta ba bugu da kari a watan da ya gabata mahaifiyar maimunan ta rasu shima ta wallafa a shafin ta jaruman Kannywood na tayi mata ta’aziyya amma Gwanjan bai mata ta’aziyya ko ya wallafa a shafin sa ba da fatan Allah yay mata rahama ba.

Advertising
Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button