Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Jaruma Hafsat Idris ta sanya Sarkar gwal ta kimanin Naira Miliyan 11 a bikin sunan jikarta

Kamar yadda kuka sania satin daya gabata ne aka yi sunan jikar jarumar masana’antar kannywood Hafsat Idris inda jikar tata taci sunan ta Hafsat Junior, sai dai shagalin bikin ya dauki hankulan matuka duba da yadda wani bikin auren ma bai kai shi jama’a ba musamman jaruman kannywood mata ba inda aka yi bisha sha sosai.

Advertising

Uwar jego tayi shoga ta kece raini inda ta sanya leshi ubansu mai matukar tsada da sarkar gwal wanda aka yi kiyasin kudin ta zai zai kai kimanin Naira Miliyan goma sha daya 11M, shafin labaran kannyood dake kan Twitter ne ya tabbatar da hakan inda ya wallafa hoton jarumar gami da wani rubutu kamar haka.

Sarkar gwal fin da jaruma.Hafsat Idris ta saka a ranar sunan jikar ta Hafsat Junior, ance kudin ta ya kai Naira Miliyan goma sha data 11M.

Allah ya kara arziki, Allah kuma ya raya mana Hafsat karama Ameen.

Advertising

Jaruman masana’antar kannywood Mata da dama sun halarci wannan gagarumin shagalin sunan irin su, Mansurah Isah, Sameerah Ahmad Aina’u, Sadiya Gyale da sauran su.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuga yadda aka yi gagarumin shagalin bikin sunan na jikar jaruma Hafsat Idris.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button