Advertising
Advertising
Labarai

Wani dan Nageriya mai suna “Ani Nnamdi Chris” ya angwance da Amaryar sa akan kudi Naira N20,500

Wani dan Nageriya mai suna "Ani Nnamdi Chris" ya angwance da Amaryar sa akan kudi Naira N20,500

Wani dan Nageriya mai suna “Ani Nnamdi Chris” ya angwance da wata kyakkyawar matar sa wanda suka shirya wani kwarya-kwaryar biki wanda aka yi taron cikin sirri.

Advertising

A lokacin a aka wallafa hotunan bikin nasu a ranar hudu ga watan Fabrairun Angwan mai suna “Ani Nnamdi Chris” ya bayyana cewa.

Duk-duk abin da ya kashe a wannan auren nasu bau wuce Naira dubu ashirin da dari biyar ba N20,500, bayan haka cikin murna da farin ciki “Ani Nnamdi Chris” ya kara bayyana yadda ya gayyaci mutane da basu wuce goma ba tare da shi da Amaryar tasa, inda yace aure bashi da tsada kawai ya danganta ne da karfin ka.

Wannan auren da “Ani Nnamdi Chris” ya yi tare da Amaryar sa ya dauku hankulan al’umma da dama, duba da yadda ya bayyana kudin da ya kashe a auren nasu wanda bai kai ya kawo ba.

Advertising

Ga hotunan auren “Ani Nnamdi Chris” tare da Amaryar sa.

Bayan wannan labarin da “Ani Nnamdi Chris” ya bayyana game da auren nasa, mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su kamar haka.

@Sammygyang ya ce: Kana da dabara. Ina taya ka murna! Kayi wa auren ka tanadi ba biki ba. Mutane da yawa suna almubazzaranci a bukukuwan su suke yi duk don su birge tarin mutanen da basa kaunar su. Amma idan auren ya lalace, kashi 80 cikin 100 na mutanen sune zasu fara gulmarsu a shagon aski da gidajen giya.

@emelda_ ani ya rubuta: Kawu na Nnamdi, kamar yadda naji dadin abinda kayi, baka bada cikakken labarin ba. Kada kasa wadan nan kananan yaran su yi tunanin dubu 30 zata ishe su aure. ” Yanzu, baka bamu labarin yadda shagalin bikin al’adan ya kaya ba. Ina da tabbacin ka biya sadakin ta.

@ejyvik yace: Ina jan kunnen aboki na da matar sa da suka sa ni na biya dubu 160 na ankon da ban sa ba, idan suka yi kuskuren nuna sun gaji da auren, su fara tunanin biya na kudi na har da riba, Ubangiji ya albarkaci gidan auren ku.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button