Advertising
Advertising
Labarai

Daga karshe dai Sheikh Abdallah Gadon Kaya ya janye kalaman da ya fada aka Likitoci

Daga karshe dai Sheikh Abdallah Gadon Kaya ya janye kalaman da ya fada aka Likitoci

Kamar yadda kuka sani dai Sheikh Abdallah Gadon Kaya ya fadi wasu kalamai akan Likitoci wanda har abin ya kai ga sun bukaci ya janye kalaman da ya fada, duba da abin daya fada zai iya martaba su da kuma kimar su tare da aikin da suke na Likitanci.

Advertising

Inda a cikin kalaman da Sheikh Abdallah ya fada kan Likitocin yake cewa, mutum sai ya bar matar sa taje tana Night Duty wato aikin kwana, amma sabida tsarin da ake kai tsari ne wanda ba na musulinci ba tsari ne na yahudanci sai a hada mace da namiji suyi aikin kwana a ofishi guda.

Dalilin wannan kalaman da ya fada Likitocin suka ji babu dadi wanda har ta kai ga sun yi magana kan cewa, ya janye wannan kalaman da ya fada a kan su.

Toa yanzu kuma mun sami wata bidiyo daga tashar “Kundin shahara” dake kan manhajar inda inda Sheikh Abdallah Gadon Kaya janye kalaman da ya fada akan Likitocin.

Advertising

Sannan kuma yake kara wayar da al’umma kai domin su gane abin da yake nufi kan kalaman da ya fada akan Likitocin, ba wai ya fadi wadannan kalaman ne domin yaci zarafin su ba.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekken bayani daga bakin Sheikh Abdallah Gadon Kaya lokacin da yake janye kalaman da ya fada akan Likitocin.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button