Advertising
Advertising
Labarai

Matsalar da za’a shiga nan gaba a Nageriya sai tafi wanda ake ciki a yanzu, cewar tsohon Sarkin Kano Sunusi

https://youtu.be/lRBg-Dvd_A0

Tsohon Sarkin Kano Muhamnad Sunusi Lamido II ya yi wani zazzafan gargadi gami da jan kunnen ‘yan Naheriya akan wani hasashe da ya yi cewa, za’a shiga wani mawuyacin hali a Kasar nan gaba fiye da wanda ake ciki a yanzu.

Advertising

Kuma bisa binciken tsohon Sarkin mummunan yanayin da za’a shiga a Kasar zai fara ne daga shekarar da za’a yi zabe, wato shekara mai zuwa ta 2023.

Haka zalika Sunusi yaja hankalin dukkan masu neman shugabancin kasar ta Nageriya cewa, suyi kyakkyawan shiri akan halin da Kasar take ciki kuna take fuskanta nan gaba.

Sunusi Lamido dai shine tsohon gwamnan babban bakin Nageriya “CBN” sannan kuma tsohon Sarkin Kano, wanda gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tsige shi daga kan kujerar mulki wanda a halin yanzu shine Khalifan Darikar na Kasar Nageriya baki daya.

Advertising

Tsohon Sarkin ya gabatar da wancan jawabi ne a lokacin da jihar Ogun dake karamar hukumar Abeokuta, inda ya halarci bikin murnar shekara tamanin da haihuwa na jagorar addini na Kasar yarbawa mai suna ” Chief Tayo Sowunmi”, wanda aka fi sani da Babanla adinni of Egbaland.

Sarki Sunusi yace, a gaskiya muna rayuwa cikin siradi a shekara 2015 muna cikin mawuyacin hali, a shekara 2023 zamu kasance cikin mawuyacin halin da yafi na shekarar 2015.

Sarki Sunusi ya kara da cewa, Ina fatan wadanda suke fafutukar zama shugabannin kasa sun fashinci cewa, matsalolin da zasu fuskanta suna da yawa sosai ninkin ba ninkin wanda muka fuskanta a shekarar 2015.

Mai martabar ya kara da cewa, dole ne dukkanninmu mu shiryawa matakai masu tsauri, kuma idan aka dauke su dukkanninmu sai mun dandana kudar mu.

Maganin abin da wai shine dukkanninmu mu tsindima a siyasa ba , wannan kasar tana bukatar ‘yan siyasa na gari.

Tana bukatar malamai na musulinci da na kirista wanda zasu iya tashi tsaye su gayawa ‘yan siyasa cewa, suji tsoron Allah, a cewar Sarki Sunusi.

Daga karshe sai mai martaba Sarki Sunusi Lamido ya karkare da cewa, tana bukatar shugabannin gargajiya wadanda zasu fadi abin dake zuciyar jama’a, kowa yana da rawar da zai taka kuma dole mu tashi tsaye muyi iya yin mu.

Advertising

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button