Labaran Kannywood

Mijina bai min saki uku ba cewar Maimuna matar Ado Gwanja matsalar mu ce ta cikin gida cewar Gwanja

Mijina bai min saki uku ba cewar Maimuna matar Ado Gwanja matsalar mu ce ta cikin gida cewar Gwanja

A jiya ne dai wani labari na jita-jita yake ta yawo a kafafun sada zumunta kan cewa, mawaki kuma jarumi Ado Gwanja ya yiwa matar sa maimuna saki uku wanda labarin ya bata zukatan masoyan sa.

Amma yanzu haka wakilin tashar “Tsakar Gida” dake kan manhajar Youtube ya sami damar zantawa da Ado Gwanja kan labarin da yake ta yawo na cewa ya saki matar sa Maimuna saki uku.

Kafin nan ma Maimuna matar Ado Gwanja ta tuntunbi wakilin tashar “Tsakar Gida” a shafin sa na instagram, inda ta bashi karin haske game da abin dake faruwa tsakanin ta da Mijin nata Ado Gwanja.

Wanda a lokacin Maimuna ta sanar masa da komai tare da cewa, komai mukaddari je daga Allah idan ma sakin da gaske ne ai kaddara ce tana kan kowa.

Sannan ta kara da cewa, ita da Mijin ta Ado Gwanja suna son junan su kawai wani tsautsayi ne ya gifta ta tsakanin su har ya sallame ta ta tafi gidan su, sannan kuma bata bayyana ko menene makasudin abin da ya kawi sabanin nash ba domin tana son Mijin nata bata son wani abu da wasu zasu zafe shi, ko ita su zage ta domin kowa da yadda zai kalli abin.

A cikin shirar da aka yi da Maimuna jaddada yadda take son Mijin ta Ado Gwanja da kuma tsoron abin da zai taba mutuncin sa ko nata, amma ta tabbatar wa da wakilin tashar “Tsakar Gida” a yanzu haka bata gidan Mijin nata tana gidan su kuma abin da ya wuce bata son yana dawowa sai dai tasan tana son Mijin ta kuma komai zai daidaita.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekkiyar shirar da walikin tashar “Tsakar Gida” ya yi da Ado Gwanja akan abin dake faruwa tsakanin sa da matar sa Maimuna.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button