Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Ali Nuhu ya karyata maganar da Ladin Cima ta fada na cewa baifi dubu biyu ake sallamarta ba a Fim

Ali Nuhu ya karyata maganar da Ladin Cima ta fada na cewa baifi dubu biyu ake sallamarta ba a Fim

Kamar yadda kuka sani a dazu mun kawo muku labari tare da bidiyon yadda wata tsohuwa mai suna Ladin Cima kuma jaruma a masana’antar kannywood, inda ta bayyana cewa.

Advertising

Tun da ta fara harkar fim har kawo yanzu ba’a taba bata wani kudi wanda zata amfani kanta ba, domin duk shirin fim din da ake da ita kudin da ake bata baiwuce dubu biyu ko uku ba, har ma ta bayyana cewa take wajan daukar wani fim amma ana gamawa aka sallame ta da naira dubu biyu.

Jaruma Ladin Cima ta bayyana hakan ne a lokacin da suka yi shira da gidan jaridar BBC Hausa, a cikin shirin nan nasu na daga bakin mai ita.

To bayan wadannan maganganu da ta fada a lokacin tattaunawar tasu da BBC Hausa sai labarin yayi ta yawo a kafafun sada zumunta, wanda har ta kai ga jarumi wanda ake masa lakabi da sarki a kannywood wato Ali Nuhu ya yi martani akan maganar da ta fada.

Advertising

Inda nan take jarumi Ali Nuhu ya karyata wannan maganar da jaruma Ladin Cima ta fada kan kudin da ake sallamar ta idan aka shirya fim da ita, inda yake cewa.

@realalinuhu_ Gani nan, ka je ka tambayeta ko nawa aka biya ta a ALAQA? I do not know why some of these elderly people keep betraying the industry just to gain people’s sympathy. Amma Allah ai yana gani kuma zai jikin ta wanda ya zalunci wani.

Ma’ana ali nuhu yace, baisan miyasa tsofaffin mutane suke a koda yaushe su kunyata masana’antar saboda kawai su samu wani tallafi.

Bayan martanin da jarumi Ali Nuhu ya yi akan maganar da jarumi Ladin Cima ta fada nan take Daraktotin masana’antar kannywood suka fara nasu martanin, inda har Darakta Aminu S Bono yake cewa.

@aminusbono: Ana gidan Badamasi Gabon tabata 300k kuma wlh a film din jammaje insearch of the King wlh voice dinta kawai aka dauka ko hotonta ba,a gani ba amma 20k maishadda yabata.

@aminusbono: toh jamaa ga Darakta ma yace wucewa kawai tayi a waka amma taja 15,000.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button