Naso nayi shuhura da sunan karuwa sai na tuna ni ‘yar Arewa ce, cewar sabuwar Salma ta Kwana Casa’in
Sabuwar Salma ta cikin shirin Kwana Casa’in 90 wanda tashar Arewa24 take haskawa wato Mufeedah, ta bayyana wani al’amari da ya hanata yin shuhura a dandalin sada zumunta na Twitter.
Mufeedah ta bayyana hakan ne a shafin ta na sada zumunta instagram cikin harshen turanci a wata bidiyo data wallafa, inda a hausance take cewa.
’Akwai wani abu dana gani da yake bani dariya tun bayan da wowar shaiin Twitter, akwai wani Hashtaga Twitter da yake ta ya wo inda a cikin awa daya mutum zai iya yin shuhura sosai.
Na so nayi amfani da wannan Hashtaga shafina ta hanyar sanya hotuna na da rubutu na, kuma sunan wannan Hashtag shine “Ashawo”.
Gaskiya na so nayi amfani dashi sabida na so nayi amfani dashi na yi suna sosai sai na tuna da cewa ‘yar Arewa ce ni, idan har nayi amfani da wannan babu wanda zai kara saurare na to sabida na zauna Iafiya na fasa amfani da
wannan Hashtaga din.
Sabida da zarar nayi tsautsayi nayi amfani dashi, InnaIiIIahi Wa’inna 113th Raji’un, a wannan rana na riga na mutu kenan.
Ga bbidiyon nan a kasa domin kuji sauran abin da take fada da bakin ta cikin harshen turanci.