Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Tunda nake harkar Fim ba’a taba bani kudin dazan taimaki kaina ba, cewar wata tsohuwa a kannywood

Wata tsohuwa a masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood wacce take fitowa a matsayin uwa, ta bayyana wani al’amari game da abin da ake biyan ta a duk lokacin da aka yi shirin fim da ita.

Advertising

Kamar yadda kuka sani gidan jaridar BBC Hausa suna tattaunawa da jaruman masana’antar kannywood a wani shirin su na daga bakin mai ita, inda jaruman suke bada tarihin rayuwar su da abin data kun sa.

To a wannan karon ma BBC Hausa sun tattauna da tsohuwar wacce iat ma jaruma ce a masana’antar kannywood, wanda a lokacin shirar tasu take bayyana cewa.

Tun da ta fara harkar fim har yanzu bata taba yin wani fim wanda za’a dauki dubu hamsin ko dubu ashirin ko talatin a bata ba bare tayi tanajin wani abu.

Advertising

Inda ta kara da cewa, idan aka yi shirin fim din da ita ana daukar dubu biyar dubu uku ko dubu biyu a bata, inda ta kara da cewa a wannan lokacin ma taje wajan da ake shirya fim din amma wallahi dubu biyu kawai aka bata.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekkiyar shirar da aka yi da tsohuwar wacce jatuma ce a masana’antar kannywood.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.

https://youtu.be/i4WhfsVnMiI

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button