Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Martanin Abubakar mai Shadda ga Sarkin waka kan mummunar maganar daya fada a kan ‘yan Fim

Martanin Abubakar mai Shadda ga Sarkin waka kan mummunar maganar daya fada a kan 'yan Fim

Kamar yadda a yanzu labarin Ladin Cima jarumar kannywood ya karade kafafun sada zumunta kan wata magana ta da fada game da kudin da ake sallamar ta a harkar fim, wanda a yanzu abin za zama cece-kuce.

Advertising

Idan baku manta ba a dazu mun kawo muku labarin yadda Naziru M Ahmad wato Sarkin Waka ya bayyana a cikin wata bidiyo, inda yake goyon bayan maganar da jaruma Ladin Cima ta fada na cewa bai fi dubu biyu ko uku ko niyar ake bata ba idan aka shirya fim da ita.

Har ma Nazir Sarkin waka yake fadin cewa, wasu matan ma ba’a sanya su a harkar fim din sai anyi lalata da su, inda ya fadi maganar cikin kwarin gwaiwa badan yana tsron abin da zai biyo baya ba.

To bayan wannan maganar da Nazir Sarkin waka ya fada na cewa, sai anyi lalata da ‘yam mata ake sanya su a harkar fim, da kuma goyon bayan maganar da jaruma Ladin cima ta fada.

Advertising

Nan take Daraktotin masana’antar kannywood suka fara maida masa da martanin abin da ta fada, wanda a yanzu muka sami wata bidiyon ficaccan Daraktan kannywood Abubakar Bashir mai Shadda, inda yake maidawa da Nazir Sarkin waka martani kan mummunar maganar da ya fada a kan su.

Abubakar mai Shadda a cikin bidiyon ya fadi cewa, duk abin da Sarkin waka ya fada akan su karya ne na cewa sai sunyi lalata da ‘yam mata sannan su sanya su a shirin fim din su.

Mai Shadda ya maida martani sosai akan Naziru Sarkin waka kan mummunar maganar da ya fada akan su.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekken martanin da Abubakar Bashir mai Shadda ya maidawa da Nazir Sarkin waka.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button