Labaran Kannywood

Nazir Sarkin Waka ya yiwa Ali Nuhu da Falalu a Dorayi kaca-kaca kan karyata maganar Ladin Cima

A shirar da BBC Hausa tayi da jarumar kannywood Ladin Cima a jiya inda ta fadi wata magana wanda ta janyo mata maganganu daga sauran jaruman kannywood irin su Ali Nuhu, Falalu A Dorayi, Aminu S Bono da dai sauran su.

Ladin Cima ta janyowa kan nata ne cece-kucen bayan da bayyana cewa, duk lokacin da aka shirya fim da ita kudin da ake biyan bai wuce naira dubu biyu ko uku ko biyar ba.

Dalilin wannan maganar da ta fada yasa jaruman kannywood din suka karya hakan, inda jarumi Ali Nuhu yake cewa.

Ka san wasu suna yi wa jama’a yadda suka ga dama ne, wani sai ka ga ya kyautata maka wani kuma ka ga bai kyautata maka ba.

Ya kamata idan mutum yana bayani ya rinƙa bambancewa ya ce wasu suna kyautata mana ya kuma ce wasu ba su yi ,” in ji Ali Nuhu.

Sannan Ali Nuhu ya kara da cewa, wannan kalaman da Ladin Cima ta fada sun janyo masa zagi daga wajan al’umma, domin fim din kwanakin nan da suka yi tare da ita.

To shine a yanzu Nazir M Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Waka ya fito cikin bacin rai ya nuna cewa, wallahi babu Allah a zukatansu sannan yace abinda tsohuwar nan ta fadi tabbas haka ake basu.

Inda yace Ali nuhu da falalu dorayi kuji tsoron Allah ku fadi gaskiya, Nazir M Ahmad wato Sarkin Waka ya fito yayi rantsuwa da Allah an yiwa tsofaffin nan haka a masana’antar kannywood.

Sarkin Waka ya yi maganganu masu yawa a cikin bidiyon daya wallafa a shafin sa na sada zumunta instagram, zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekken bayani daga bakin sa.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.

https://www.instagram.com/tv/CZz5GPLK-Vb/?utm_medium=copy_link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button