Labaran Kannywood

Yanzu yanzu Nuhu Abdullahi ya fadi dalilin dayasa ya dena fim din Labarina.

A dai dai lokacin da rikici ke barkewa tsakanin Naziru Sarkin waka da Jarumi Ali Nuhu kan Rikicin wata jaruma da tace ba’a taba biyanta kudin aiki a masana’antar ba sama da naira 2000 ba.

Matar wadda ake kira Da Hajiya Cimma ta fadi haka ne a wata hira da gidan jaridar BBC Hausa sukai da ita inda tace ba’a taba bata sama da 2000 ba kudin aiki. Hakan yasa jarumi Ali Nuhu ya karyata maganar tata yace da hanun sa ya biyata naira 40,000, Shima Falalau A Dorayi yace yabiyata kudi fiye da haka haka sauran Furodusoshi sun fadi haka.

A dazu jarumi nuhu Abdullahi yayiwa Naziru Sarkin waka raddi kan maganar daya fada Na cewar babu Allah a ran manyan jaruman Masana’antar kan cewar da sukai basu san ana biyan Ladin Cimma N2,000 a matsayin kudin aiki ba.

Nuhu Abdullahi ya ce sam mawakin bai yiwa jaruman adalci ba inya bukace shi da ya karkata wa’azin nasa ya hada harda dan uwansa kaman yadda zaku gani anan kasa.

Nuhu Abdullahi

Jan hankali; Akwai bukatar duk lokacin da mutum zai yi magana ya yi adalci, Falalu Dorayi da Ali Nuhu sun ce ga yadda suke biyan Mama Tambaya kudin aiki, BBC Hausa ta tabbatar da hakan wurin ta. Naziru kafito ka yi kudin Goro baka kyauta ba. Sai ka yi musu adalci da ire-iren su da su ke biyan hakkin aiki Yadda Yakamata. Wadanda kuma basa biyan hakkin mutane idan anyi mu su aiki harda “Dan’uwan ka” yana ciki sai kacigaba da yi mu su wa’azi, Allah ya shirye su!

Wannan magana da jarumi Nuhu Abdullahi ya fada yasa ake ganin cewar rashin biyan sa hakkin sane yasa ya dena fitowa a cikin shin na labarina.

https://www.instagram.com/p/CZ1NoNFMW6I/?utm_medium=copy_link

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button