Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Ali Artwork ya goyi bayan maganar da Naziru Sarkin waka ya fada akan ‘yan Kannywood

Ali Artwork ya goyi bayan maganar da Naziru Sarkin waka ya fada akan 'yan Kannywood

Kamar yadda kuka sani dai a shekaran jiya ne dai jarumar kannywood Ladin Cima ta bayyanawa al’umma kudin da ake sallamar ta a harkar fim, wanda har tace duka-duka kudin da ake bata bayya wuce naira dubu uku ko biyar.

Advertising

Ladin Cima ta bayyana hakan ne a lokacin da suka shira da gidan jaridar BBC Hausa a shirin su na daga bakin mai ita, wanda hakan ya janyo cece-kuce a masana’antar kannuwood wasu suna goyon bayan ta wasu kuma suna fadin aibun abin data bayyana.

To bayan wasu daga cikin jaruman kannywood din sun nuna rashin din dadin su kan maganar da Ladin Cima ta fada, sai abin da yaka tabarbarewa wanda har Nazir Sarkin waka ya wallafa bidiyo a shafin sa na instagram yana goyon bayan maganar da Ladin Cima ta fada.

A cikin maganganun da Naziru Sarkin waka ya fada sun kara tada kura inda yake cewa, wasu matan ma sai anyilalata da su sannan ake saka su a harkar fim.

Advertising

Bayan wannan maganar da ya yi nan take Darakta Abubakar Bashir mai Shadda ya bayyana a cikin bidiyo yana maida masa da martani.

Ba tare da bata lokaci ba sai muka ga jarumin barkwancin nan mai shirya Comedy wato Ali Artwork, shima ya wallafa bidiyo yana goyon bayan maganar da Naziru Sarkin waka ya fada.

Wanda har ya yi wasu maganganu kan mudin aikin sa da jarumi Ali Nuhu ya cinye masa bayan ya masa wani aikin Editing.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji maganganun da Ali Artwork yake fada wanda hakan yake nuna cewa, yana goyon bayan maganar da Naziru Sarkin waka ya fada.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button