Duk wanda zai taba mana sana’a sai mun taba shi ko wanene martanin Lawan Ahmad ga Naziru Sarkin waka
Lawan Ahmad wanda aka fi sani da Umar Hashim a cikin shirin nan mai dogon zango wanda tashar Bakori Tv dake kan manhajar Youtube take haskawa wato, ya yi martani akan maganar da Naziru Sarkin waka yake fada a cikin wata bidiyo yana cewa ana lalata da ‘yam mata kafin a sanya su a cikin fim.
Wannan maganar ta Naziru Sarkin waka jarumai da dama na masana’antar kannywood sun yi martani akan ta, wanda a farko Abubakar Bashir mai shadda ya fara maida masa da martani.
To shi ne Lawan Ahmad jarumin shirin Izzar so yaga abin ya yi masa zafi inda shi ma ya wallafa wani rubutu a shafin na sada zumunta instagram yana martani akan wannan maganar ta Naziru Sarkin waka, inda a cikin rubutun nasa yake cewa.
Kannywood tayi mana riga tayi mana wanda kuma kaima tayi maka komai sabida ko waka kake yi sai ka rabi kannywood sannan zakai inda kake so, sabida haka duk wanda yaci mutuncin sana’ar mi sai inda karfin mu ya kare Ehe.
Wannan shi ne rubutun da jarumin Izzar so Lawan Ahmad ya wallafa a shafin sa na instagram, domin ya nuna bacin ran sa ga maganar da Naziru Sarkin waka ya fada a kan su.