Advertising
Advertising
Labarai

Za’a fara yiwa Mata masu juna biyu goma ta arziki a jihar Jigawa domin kula da lafiyar ‘yayan dake cikin su

Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana cewa, ta kammala shirin ta tsaf domin fara biyan mata masu juna biyu akalla guda budu biyar 5,000 da aka dauki bayanan su wanda za’a ana basu alawus din N5,000 a kowane wata.

Advertising

Mataimakain Gwamanan Jihar Jigawa Mallam Umar Namadi, shi ne ya bayyana hakan yayin wata zantawar sa da manema labarai a Dutse babban birnin Jihar ta Jigawa.

Jihar ta samar da shirin ne domin taimaka wa mazauna yankunan karkara su rika zuwa awon ciki da kuma zuwa asibiti domin haihuwa, kamar yadda Aminiya ta ruwaito

Mataimakin gwamnan Malam Umar Namadi ya kara da cewa, tuni gwamnati ta sanya shirin a cikin kasafin kudinta na shekarun 2021 da 2022.

Advertising

Ya kara da cewa, suna sa rana kudaden zasu taimaka wa matan wajen sayen abincin da zai inganta lafiyar su da ta ‘yayan dake cikin su sabida kare su daga kamuwa da cutar yunwa.

Malam Umar Namadi ya kara da cewa, tuni aka bude wa kimanin mata dubu uku da dari takwas 3,800 asusun ajiya na banki, kuma za’a fara biyan su a watan Fabrairun 2022, yayin da suke kokarin magance matsalar da ta shafi sauran ragowar mata dubu daya da dari biyu1,200.

Mataimakin gwamnan bai tsaya nan ba ya kara da cewa, an zabo matan ne daga mazabun siyasa dari biyu da tamanin da bakwai 287 na Jihar, domin fara shirin a matsayin gwaji kafin daga bisani a fadada shi da zarar wannan ya sami nasara.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button