Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Bayan cece-kucen da ake akan maganar da Ladin Cima ta fada Misbahu M Ahmad ya tofa albarkacin bakin sa

Misbahu M Ahmad wanda dan uwa ne ga mawaki Naziru M Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin waka, shi ma ya fito ya tofa albarkacin bakin sa akan masu kalubalantar maganar da Ali Nuhu, Falalu A Dorayi suka yi, a lokacin da Ladin Cima ta bayyana cewa ba’a bata kudi sama da dubu biyu ko uku a fim.

Advertising

A cikin bidiyon da Misbahu M Ahmad ya wallafa a shafin sa na sada zumun ta instagram ya fara da cewa.

Yan uwa ina son in dan ja hankali ko in bada
shawara a bisa nasiha ‘yan jarida sun buga balarin Ladin Cima wanda uwa ce kaka ce a cikin wannan masana’antar, tayi bayyani akan wasu abubuwa da take gani ko tasani ko a’a abun nan ya fito daga bakin dan jarida domin yayi amfani da hikimarsa wajen yada Iabarin da yake so.

To amma naga wasu sun kauce hanyar ko sun
dauki Iayin tona mata asiri wannan yace ya bata
kaza wannan yace ya bata kaza to Iadin cima ae
uwa ce kaka ce a wannan masana’antar, bai
kamata ba wanda kasan wani naka ko tsohonka
ko kakanka bazai fito yayi magana ba ka flto ka
karyata shi.

Advertising

To karkayiwa kakan wani to yakamata koda fada
tayi ana ganin abun ba haka yake ba ko ba dai dai bane to mu ’yayane mabiya, muyi hakuri muyi mata shuru yafi banda dalilin mutane ne zasu fara hawa kan kafafensu na sada zumunta ba suna na taba dubu kaza ae ko nawa kaba Ladin Cima baka biyata ba.

Matsalar ku kenan sufa su Ali Nuhu da Falalu A Dorayi basu ce baa baiyan haka bah su dai sunce sun bata dubu ashirin,da dubu arbain a aikin da sukayi da itah.

Zaku iya kallon bidiyon da Misbahu M Ahmad ya wallafa a shafin nasa na sada zumunta instagram, domin kuji cikekken bayani daga bakin sa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button