Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Jaruma Maryam Yahaya ta tafi yawon shakatawa kasar Dubai bayan jikin ta ya kara sauki

Ficacciyar jarumar masana’antar kannywood Maryam Yahaya ziyarci hadaddiyar daular Larabawa wato kasar Dubai, inda ta wallafa hotunan a shafin na sada zumunta instagram.

Advertising

Maryam Yahaya dai ta kwanta rashin lafiyar da jikinta ya jigata sosai wanda har yayin ta ya saura, amma cikin ikon Allah da Rahamar sa a yanzu ta sami sauki wanda har ta fara tafiya yawon buda ido.

Jaruma Maryam Yahaya ta wallafa zafafan hotuna da bidiyo wanda suka dauki hankulan mabiyanta na shafin ta instagram, inda wasu suka rinka yaba hotunan nata wasu kuma suke kara bata shawara akan ta sake ragewa abin da ake ta jira ta sake samin sauki.

Ga hotunan na a kasa domin ku kalla.

Advertising

Bayan wadannan zafafan hotunan da ta wallafa sai kuma ta sake daukar wata bidiyo tana shakatawa yadda ran ta yake so, wanda hakan yake nuna cewa a yanzu ta sake samin sauki fiye a da.

Ga bidiyin da ta wallafa a kasa domin ku kalla.

https://www.instagram.com/p/CZ5xTkvhUDB/?utm_medium=copy_link

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button