Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Jarumi Sani Indomie ya maidawa da Naziru Sarkin waka maganar da ya fada a kan su ta yin lalata da ‘yan mata

Shi ma ficaccan jarumi kuma Furodusa a masana’antar shirya fina-finai ta kannywood Sani Indomie, ya yi raddi akan maganar da Naziru Sarkin waka ya fada kan cewa sai an yi lalata da ‘yam mata ake sanya su a shirin fim.

Advertising

Da farko dai jarumi Sani Indomie ya yabawa Darakta Abubakar Bashir mai Shadda kan biyan kudin aiki da yake a duk lokacin da aka yi shirin fim, domin baya bari kudin mutum ya jima a wajan sa balle ma ya hana shi.

Sannan kuma Sani Indomie ya kara jinjinawa Abubakar Bashir mai Shadda akan yunkurin kare masana’antar kannywood da ya yi, kan maganar da Naziru Sarkin waka ya jefe su da ita na yin lalata da ‘yam mata kafin a sanya su a harkar fim.

Bayan haka ya sake dawowa kan Naziru Sarkin waka yana maida masa da martanin mummunanr maganar da ya fada a kan su.

Advertising

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domi kuji martanin da jarumi kuma furodusa a masana’antar lannywood Sani Indomie ya maidawa da Naziru Sarkin waka.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button