Labaran Kannywood

Yanzu-yanzu: Naziru Sarkin waka ya yi nadamar mummunar maganar daya fada akan ‘yan kannywood

Yanzu-yanzu: Naziru Sarkin waka ya yi nadamar mummunar maganar daya fada akan 'yan kannywood

Yanzu-yanzu Naziru Sarkin waka ya bada hakuri a bangaren kannywood kan mummunar maganar da ya alakan nasu da ita na cewa, sai anyi lalata da ‘yam mata sannan ake san ya su a shirin fim.

Bayan cece-kucen da wasu Daraktoti da jarumai na masana’antar kannywood suka sha yi akan Naziru Sarkin waka kan maganar da ya alakan tasu da ita, wanda a yanzu abin ya karade kafafun sada zumunta.

To a yanzu kuma sai mawaki Naziru M Ahmad ya sake wallafa wata bidiyo a shafin sa na sada zumunta instagram inda yake mai daba hakuri akan maganar da ya fada.

Sannan kuma ya kara da cewa, bai fadi wannan maganar ne domin ya bafawa wani sana’ar sa ba.

Hausawa dai suna cewa waka a bakin mai ita tafi dadi, zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekken bayani daga bakin Naziru Sarkin waka.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

https://www.instagram.com/tv/CZ6-JW3qkKg/?utm_medium=copy_link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button