A zaman Kotun a yau Litinin: Abdulmalik Tanko ya fadi cewa bashi ya aikata mummunan kisa akan Hanifa ba
A zaman Kotun a yau Litinin: Abdulmalik Tanko ya fadi cewa bashi ya aikata mummunan kisa akan Hanifa ba
Abdulmalik Tanko wanda ake zargin ya yi garkuwa da karamar yarinya ‘yar jihar Kano mai shekaru biyar wato Hanida, sannan ya yi mata kisan gilla ta hanyar bata guda kuma daddatsa sassan jikin bayan ta mutu.
Abdulmalik Tanko tare da shi da sauran wadanda suka yi aika-aikar, Hashimu Isyaku da Fatima Jibrin, sun musanta cewa basu aikata wannan mummunar aika-aikar na.
A yau Litinin ne a ka sake kawo Abdulmalik Tanko tare da abokan aikata laifin da a ke zargi su, Hashimu Isyaku da Fatima Jibrin a gaban Babbar Kotun jihar Kano karkashin Alkali Usman Na-Abba.
Amma bayan da aka karanto musu tuhume-tuhumen da ake musu sai suka musanta, da ake tuhumar Abdulmalik Tanko kan cewa ya yi garkuwa da Hanifa sannan kuma ya kashe ta sai yake cewa, bai aikata ba kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
Amma zuwa nan gaba zamuji sauran bayanin inda aka kwana.