Wasu da ake zargin ‘yan fashi ne sun shiga har gidan wata Mata sun kashe ta tare da raunata ‘yayan ta
Har yanzu dai al’amuran ta’addanci kara tsamari yake inda ake ta kashe mutane babu gaira babu dalili, wanda a yanzu haka muka sami labarin wata mata da ‘yan tashi suka shiga har cikin gidan ta suka kash ta.
Wasu mutane da ake zargin ‘yan fashi ne sun shiga har gidan wata mata mai suna Rukayya sun hallaka ta tare da jiwa ‘yayan ta biyu raunika.
Al’amarin ya matukar tayar wa da mutane hankali duba yadda babu wanda ya san lokacin da ‘yan fashin suka shiga har gidan matar sannan suka kashe ta tare da jiwa ‘yayan nata raunika.
Sai dai kuma ana kyautata zaton ‘yan fashin sun shiga gidan matar ne bayan sallar magaruba inda a lokacin suka yi wannan aika-aikar.
Duk da cewa mazauna unguwar sun ki yarda ina BBC ta dauki muryoyinsu inda suka bayyana cewa, akwai magina a jikin gidan da shagunan sayar da kayayyaki haka kuma a iya saninsu ba suga shigar wani bako gidan ba, haka kuma ba suga fitar mutanen da suka aikata kisan kan ba.
Sai bayan da maigidanta ya dawo ne sannan aka san halin da ake ciki inda ake zargin da tabarya suka daki matar a kai har wuri biyu, sannan suka daki danta a kansa sau daya sai kurjewa da aka samu a fuskar wadda take shayarwa.
Amma mijin matar da aka yi aika-aikar ya kasa yin magana sabida halin da yake ciki, wanda a yanzu haka babu kowa a gidan marigayiyar kuma ana zaman makoki a gidan iyayen marigayiyar dake Unguwar Madatai a cikin birnin Kano.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta bayyana cewa, tana gudanar da bincike kan lamarin.