Yanzu-yanzu: Rundunar ‘yan sandan kasar Nageriya ta kama DCP Abba Kyari
Yanzu-yanzu: Rundunar 'yan sandan kasar Nageriya ta kama DCP Abba Kyari
Rahotanni sun bayyana cewa, rundunar ‘yan sandan kasar Nageriya ta kama mataimakin kwamishinan ‘yan sanda “DCP Abba Kyari”.
Kamar yadda a cikin rahotannin aka bayyana cewa, yanzu haka ana tsare da “DCP Abba Kyari” a sashin tattara bayanan sirri na rundunar dake babban birnin tarayya Abuja.
Amma Kawo yanzu rundunar ‘yan sandan kasar ta Nageriya ba ta fitar da sanarwa kan batun ba, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Kamar yadda wasu daga cikin ku suka sani a ranar Litinin ne hukumar yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi ta kasar Nageriya wato “NDLEA”, ta bayyana cewa tana neman dan sanda “DCP Abba Kyari” ruwa a jallo kan zargin safarar miyagun kwayoyi.
Wanda a watan Yuli shekara ta 2021 ne rundunar ‘yan sanda ta kasar Najeriya ta dakatar da “DCP Abba Kyari” mai mukamin kwamishinan ‘yan sanda, bisa zargin karbar cin hanci daga Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppid mutumin da ke tsare a kurkukun Amurka bisa zargin damfarar miliyoyin daloli.