Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Alkawari ya cika: Naziru Sarkin waka ya turawa Ladin Cima Naira Miliyan biyu kamar yadda ya yi alkawari

Alkawari ya cika: Naziru Sarkin waka ya turawa Ladin Cima Naira Miliyan biyu kamar yadda ya yi alkawari

Alkawari ya cika ficaccan mawakin masana’antar kannywood Naziru M Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin waka, ya cika alkawarin da ya dauka nabaiwa jarumar Ladin Cima naira Miliyan biyu.

Advertising

Idan baku manta ba dai a lokacin da Ladin Cima tayi shira da gidan jaridar BBC Hausa a shirin su na daga bakin mai ita wanda suka saba yi da jaruman kannywood, ta bayyana wasu al’amru game da rayuwar ta har ta bayyana cewa tun farkon fara harkar fim din ta har kawo lokacin ba’a taba data kudi mai yawa ba sai dai naira dubu biyu ko uku ko biyar.

Wannan maganar ta Ladin Cima ta sa wasu daga cikin Daraktoci kuma jarumai a kannywood suka tofa albarkacin bakin su kan abin da ta fada.

Bayan sai mawaki Naziru M Ahmad ya wallafa wata bidiyo a shafin sa na sada zumunta instagram yana mai goyon bayan maganar Ladin Cima, har ya fadi wasu kalamai wanda suka kara tada kura a kannywood din.

Advertising

To a cikin bidiyon da Naziru Sarkin waka ta wallafa a shafin nasa ya yi alkawarin cewa, zai baiwa Ladin Cima kyautar naira Miliyan biyu domin tayi dari.

Wanda har yace idan na abinci ne yake kawowa Ladin Cima masana’antar kannywood to zai bata kyautar naira Miliyan biyu.

To a yau kuma Allah ya yarda mawaki Naziru Sarkin waka ya cika alkawarin da ya dauka na baiwa Ladin Cima naira Miliyan biyu.

To Alhamdulillahi wannan shine risit na cewa an turawa Ladin Cima naira miliyan biyu a asusun bankinta wanda Naziru Sarkin waka ya yi mata alkawari.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button