An yi zaman hulsu na ‘yan kannywood an sami daidaito kan rigimar data barke a kwanan nan
An yi zaman hulsu na 'yan kannywood an sami daidaito kan rigimar data barke a kwanan nan
Rahotanni sun bayyana cewa, an yi sulhu tsakanin jaruman masana’antar kannywood da mawaki Naziru M Ahmad wanda shima dan kannywood din ne, bayan wata hatsaniya data kaure a tsakanin su kan wata magana da Sarkin waka ya fada aka kan su.
Kamar yadda Rahotan yace tsofaffin jaruman Kannywood din irin su Kabiru mai Kaba da Ibrahim Mandawari da Shugaban MOPPON Ahmad Sarari, sune suka jagoranci kwamitin sulhun.
Kamar yadda muka sami rahotannin, tsofaffin jaruman ne suka shiga maganar ganin cewar rigimar tana nema ta wuce gona da iri, sabida haka ne suka yi gaggawar yin sulhu a tsakanin jaruman.
Bayan haka an ruwaito cewa, an yi sulhun ne a gidan mawakin Naziru M Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin waka, a jiya Litinin da Magaruba kuma a dukkan alamu an daidaita tsakanin ‘yan kannywood din.
A lokacin zaman Sulhun akwai Naziru Sarkin waka da Abubakar Bashir Mai Shadda da Mustapha Badamasi na Baraska da Musbahu Ahmad da Hadiza Mohammed da jagororin sulhu da kuma sauran masu ruwa da tsaki.
Ga hotunan lokacin da aka yi sulhu a tsakanin ‘yan kannywood din.