Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Naziru Sarkin waka ya cika alkawarin da ya dauka na baiwa Fati Slow Naira Miliyan daya 1M

Naziru Sarkin waka ya cika alkawarin da ya dauka na baiwa Fati Slow Naira Miliyan daya 1M

Kamar yadda kuka sani Naziru Sarkin waka ya wallafa wata bidiyo inda yake cewa, zai baiwa Fati Slow da kuma Ladin Cima wacce aka fi sani da Tambaya kyautar kudi, inda yace zai baiwa Fati Slow naira Miliyan daya ita kuma Ladin Cima zai bata naira Miliyan biyu.

Advertising

To sai kuma a yau muka sami wata wallafa a shafin sada zumunta na tsohuwar jarumar masana’antar kannywood Mansurah Isah, inda ta bayyana cewa har sarkin waka ya tura kudin fati slow a cikin asusun today life foundation.

inda tayi wallafa a shafin nata kamar haka.

Assalamu alaikum. Malam @naziru_sarkinwakar_san_kano ya aiko da Naira Miliyan daya cikin account din @todays_life_foundation domin mu taimakawa Fatima ( Fati slow ) juyawa.

Advertising

Yace ya yarda da Mindset dinmu kuma ya yarda zamuyi Mata abinda ya dace.

Fatima Tana godiya Kwarai dagaske.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button