Labarai

Wani matashi ya yi yunkurin kashe kan sa ta hanyar shan guda sabida Budurwar sa ta juya masa baya

Wani matashi ya yi yunkurin kashe kan sa ta hanyar shan guda sabida Budurwar sa ta juya masa baya

Kamar yadda kuka sani har yanzu dai ana samin matasan da suke yunkurin hallaka kan su dalilin budurwa, wanda a yanzu muka sami wani labarin marar dadi inda wani matashi ya yi yunkurin kashe kan sa ta hayar shan guba.

Kamar yadda muka sani rahoton cewa, wani saurayi ya yi yunkurin kashe kan sa ta hanyar shan guda, sabida masoyiyar sa ta juya masa baya.

A yau din nan ne da yamma matashin mai suna Tijjani Abubakar dan asalin unguwar Gama PRP dake yankin karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano, ya yi yunkurin kashe kan sa bayan da budurwar sa ta yaudare shi.

Matashin dan kasuwa ne yana sayar da wayar hannu ta Farm Centre ya yi wannan yunkurin ne bayan budurwar da ya shirya angoncewa da ita tace a kai kasuwa, domin ta samu wanda ya fishi iya tattali da soyayya baya ga makudan kudade da yake kashe mata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button