Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Dama ni ba dan Kannywood ba ne mutane ne kawai suke mana kudin goro, cewar Naziru Sarkin waka

Dama ni ba dan Kannywood ba ne mutane ne kawai suke mana kudin goro, cewar Naziru Sarkin waka

Ficaccan mawakin siyasa Naziru M Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin waka ya bayyana cewa, shi dama tun asali ba dan kannywood ba ne kawai dai mutane ne suke musu kudin goro da ‘yan kannywood din.

Advertising

Naziru ya bayyana haka ne a cikin wani hoton bidiyo da ya saki a shafin sada zumunta inda ya ke bada hakuri game da al’amarin da ya faru wanda har ake cece-kuce da maganarsa da yayi akan Ladin Cima ta jawo.

Sannan kuma Naziru Sarkin waka ya fadi cewa, sai dai ayi hakuri da abin daya fada domin idan gaskiya tazo bai san lokacin da yake fadan ta ba, shi dama haka yake.

Inda ya kara da cewa, dama shi ba dan masana’antar kannywood ba ne kawai dai mutane ne suke daukan haka har ma suke musu kudin goro shi da ‘yan kannywood din.

Advertising

Daka karshe kuma ya bayyana kyautar da ya bada ga Ladin Cima wacce aka fi sani da tambaya domin ta fara sana’a.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button