Advertising
Advertising
Labarai

Mawakin Kudanci Davido ya cika alkawarin da ya dauka na rabawa gidajen Marayu Naira Miliyan 250M

Mawakin Kudanci Davido ya cika alkawarin da ya dauka na rabawa gidajen Marayu Naira Miliyan 250M

Shahararran mawakin nan na kudancin Nageriya David Adeleke wanda aka fi sani da Davido a wannan lokacin ya cika alkawarin da ya dauka ra raba Naira Miliyan dari biyu da hamsin 250M ga gidajen marayu a fadin kasar nan.

Advertising

Kamar yadda wasu daga cikin ku suka sani a karshen shekarar 2021 ne mawaki Davido ya dauki alkawarin cewa, zai raba zunzurutun kudade har Naira Miliyan dari biyu da hamsin 250M ga gidajen marayu na fadin kasar Nageriya, domin murnar zagayowar ranar haihuwar sa.

Mawaki Davido ya bayyana hakan ne a wata sanarwa daya wallafa a shafin sa na sada zumunta Twitter a jiya Talata da daddare.

Inda mawaki Davido ya bada cikakken bayani da sunayen gidajen marayun da suka amfana da tallafin nasa da ya bayar, inda yake cewa gidajen marayu dari biyu da casa’in da biyu 292 ne suka amfana.

Advertising

Sannan kuma Davido ya yi godiya kan yabawar da ‘yan kwamitin da ya kafa su raba tallafin, inda yace kwamiti ne cike da mutane zakakurai dasu ka iya aiki.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button