Advertising
Advertising
Labarai

Wani magidanci ya saki Matar sa bayan yaga bidiyon ta a TikTok wanda ta dauka tun kafin suyi aure

Wani magidanci ya saki Matar sa bayan yaga bidiyon ta a TikTok tun kafin suyi aure

Kamar yadda kuka sani dai dandalin TikTok ya zama wajan lalata tarbiyyar ‘yam matan hausawa, musamman a wannan lokacin da muke ciki domin zaka ga ‘yam mata suna wallafa bidiyoyin da basu dace ba.

Advertising

To a yau kuma mun sami wata wallafa a shafin shahararran marubucin nan Datti Assalafiy na instagram, inda ya wallafa labarin wata mata da ta sanya bidiyon ta a dandalin TikTok kafin ayi auren ta amma bayan auren ta sai mijin ta ya ga bidiyon dalilin haka ya sake ta.

Datti Assalafiy ya wallafa labarin kamar haka.

TlK-TOK : mijina ya sake Ni bayan na wallafa video na a Tik-tok, wata mata ta Roki gidan talabijin din ATP Hausa domin su janye video ta, wanda su dauka a shafln ta na Tik-tok lokacin tana budurwa, sama da shekara daya, lokacin kafln tayi aure, a cikin video matashiyar tayi magana akan auren Wuff, ta nuna irin illar dake cikin auren Wuff.

Advertising

Gashi nan kamar yadda kuke gani a Screenshot, Allah ya tsare mu daga danasani, Don Girman Allah ku taya mu yadawa ko Allah zaisa ya zama darasi ga Yan baya.

https://www.instagram.com/p/CaCd_iroL5Z/?utm_medium=copy_link

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button