Wasu matasa a India sun nemi sai an hana mata sanya hijabi da dankwali a wata makaranta
Wasu matasa a India sun nemi sai an hana mata sanya hijabi da dankwali a wata makaranta
Wani rikici ya kaure a kudancin India kan hana dalibai mata sanya hijabi wanda har abin ya tsallaka zuwa Uttar Praddesh, inda wasu matasa suka yi gangami domin wata makaranta ta hana mata sanya hijabi.
A makon da ya gabata ne mahukunya suka rufe a karnataka dake kudancin India bayan da aka billo da wata sabuwar doka ta hana mata sanya hijabi da dan kwali a cikin aji.
lamarin ya haifar da bore da ga dalibai Musulmai, inda su kuma dalibai ‘yan addinin Hindu suka yi zanga-zanga ta maida martani.
Musulman wanda yawan da suke da shi kawai kashi sha uku ne 13 a kan yawan yan addinin Hindu da ya kai biliyan 1.3 na al’ummar kasar India, sun yi korafin cewa ana gallaza musu da nuna musu bambanci.
A Uttar Pradesh da ke arewacin India kuma boda da New Delhi, wani gungun matasa sama da dozin biyu sun je makarantar Dharma Samaj College a lardin Aligarh a ranar Litinin, inda su ka mika takardar yarjejeniya kan cewa a hana mata sanya hijabi kwata-kwata.
Shugaban makarantar mai suna Mukesh Bharadwaj yace, sun saba su na sanya kyalle a wuyan su irin wanda Hindu suke saka wa, inda ya kara da cewa shi bai gane mutanen ba.
A halin yanzu an hana sanya riguna na addini a ajujuwa, sai dai a wani gurin daban.
Gaskiya 2k tayi albarka 😁kalli sabbin motocin jaruman kannywood mata na milliyoyin nairori a sabuwar shekarar nan
https://youtu.be/Q46wOmscsc0