Advertising
Advertising
Labarai

Ahmad Musa ya baiwa tsohon dan wasan kwallon kafa na Super Eagles “Kingsley Obiekwu” kyautar Naira Miliyan 2

Ahmad Musa ya baiwa tsohon dan wasan kwallon kafa na Super Eagles "Kingsley Obiekwu" kyautar Naira Miliyan 2

Ahmad Musa ficaccan dan wasan kwallon kafa na Nageriya “Super Eagle” ya baiwa tsohon dan wasan kwallon kasa na “Kingsley Obiekwu” tallafin Naira Miliyan 2.

Advertising

A lokutan bayan ne dai “Kingsley Obiekwu” wanda da shi Nijeriya ta lashe gasar “Olympic” ta Atalanta 96, ya baiyana cewa.

Yana fama da matsin rayuwa inda motar shi kwaya daya tak yake haya da ita domin ya kula da iyalinsa.

Sannan kuma tsohon dan wasan wanda ya buga a kungiyoyin kwallon kafa na Rangers International dake Enugu da Udoji United, yace ya shiga harkar hayar mita ne sabida matsin rayuwa.

Advertising

Hakan ne ya sanya Ahmed Musa ya tausaya masa, inda ya bashi tallafin Naira Miliyan 2, ‘yan Nijeriya da dama ne su ka rika godewa da yaba wa Ahmed Musa ta kafafen sadarwa kan kan kyatar kudin da ya yiwa Kingsley Obiekwu.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button