Advertising
Advertising
Uncategory

Wani dalibin jam’i yace yana goyan bayan ASUU akan wannan yajin aikin da suke.

Cikin wani bayani da wani dalibin jami’a Mai suna Sunusi ya wallafa kaman haka.

Advertising

Ina Goyon bayan ASUU Amma Daiā€¦ Daga lokachin dana shiga jami’ar Bayero ta Kano (BUK) a shekarar 2009 a matsayin dalibin remedial zuwa lokachin dana fara karatun digiri a 2010 ASUU sunyi yajin aiki da yawa tsakanin na gargadi wanda baya wuce sati biyu zuwa na sai baba ta gani.

Ina dalibin level 100, muna jarabawar GSP akazo akace mu tashi ASUU sun tafi yajin aiki, jarabawar da bamuyi ba kenan, sannan mafi tsawon yajin aikin da ASUU sukayi lokachin ina dalibi shine na 2013 lokachin muna final year (level 400), saida mukayi wata shida muna zaune agida.

Tunda ASUU suke yajin aiki bantaba goyon bayan gwamnati ba kuma bantaba jin araina ya kamata ASUu su janye yajin aikin da suke ba koda gwamnati batayi musu abinda suke soba, har wanda akayi wata shida kuma muna final year banji cewa ya kamata su janye ba.

Advertising

A farkon wannan shekarar ta 2022 na koma makaranta domin yin karatun postgraduate kuma ko ayau Juma’a ya kamata ace yanzu haka ina aji ina daukar darasi amma yajin aikin ya hana hakan faruwa.

Saidai fa maganar gaskiya har yanzu ina kan bakana na goyon bayan ASUU akan yajin aiki domin maganar gaskiya idanma don kansu sukeyi sun cancanta don wani lokachin har tausayin lecturers nake wallahi balle ma nidai naga amfanin yajin aikin nasu, misali ni dalibin kimiyane (science), abaya a BUK old site inda twin theatres suke (theatre 1 & 2) babu wani gini a kusa dasu sai kasuwa, yajin aikine ya samar da duk wani gini dake gurin chiki harda central Lab da sauransu tunda gashinan ajikinsu an rubuta tetfund baro baro.

Amma sai nake ganin kamata yayi ASUU su chanja salonsu tunda ba abinda hakan keja musu banda zagi daga wayanda suke ganin dansu sukeyi, idan akan hakkinsune sunada ikon yin yajin aiki tunda haqqi ake magana amma indai wani abune wanda ba wannan ba subar gwamnati tayi duk abinda takeso chiki harda privatisation, student studies loan da sauransu, ina ganin hakan zaifi domin ita gwamnati ba damuwarta karin kudi lecturers bane, a’a biliyoyin kudade da ASUU take cewa a ware domin raya jami’o’i shine damuwarta.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button