Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Abin da yasa na baiwa Fati Slow Miliyan 1 wani Hadisin Annabi S.A.W na tuna, cewar Naziru Sarkin waka

Abin da yasa na baiwa Fati Slow Miliyan 1 wani Hadisin Annabi S.A.W na tuna, cewar Naziru Sarkin waka

Ficaccan mawakin masana’antar kannywood Naziru M Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin waka, ya bayyana dalilin da yasa ya yiwa Fati Slow kyautar da kowa ya yi mamaki.

Advertising

Sarkin waka yake cewa, ya tashi daga barci kawai sai yaji ana rade-rade akan maganganun da Fati Slow ta fada a kan sa, har ma wasu suke bashi shawarar ya hukunta ta.

Sai Naziru Sarkin waka yake cewa, wani hadisin Manzon Allah Muhammad (SAW), ya bijiro masa wanda da shi ya yi amfani ya baiwa Fati Sllow kyautar naira Miliyan daya, sabida gundarin wannan hadisi na Annabi Muhammad S.A.W yana cewa:

Ku ji tsoron Allah SWT a duk inda ku ka samu kan ku, ku biyo aikin sharri da na alheri, na alherin zai shafe sharrin, ku mu’amulanci mutane da kyakkyawan dabi’a

Advertising

Abu Dharr da Mu’adh Jabal suka ji wannan hadisi daga bakin Annabi SAW. Tirmidhi ya inganta hadisin a littafinsa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button