Labarai

Kotu ta yankewa tsohon babban Akanta na hukumar Alhajai hukuncin shekaru 7 a giyan yari dalilin almundahanar naira N73.7M

Kotu ta yankewa tsohon babban Akanta na hukumar Alhajai hukuncin shekaru 7 a giyan yari dalilin almundahanar naira N73.7M

A ranar goma sha shida 16 ne dai aka yankewa “Kawu Chindo” tsohon babban Akanta na hukumar Alhajai ta jihar Bautsi, tare da wani ma’aikacin ofishin Akanta mai suna “Ali Baba” hukincin shekaru bakwai 7 da kuma watanni uku a gidan Yari.

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito cewa, mai Sharia “Mu’azu Abubakar” na Babbar Kotun jihar Bauchi shi ne ya yanke musu hukuncin bayan da Hukumar yaki da Cin-hanci da Rashawa wato “EFCC” ta yankin jihar Gombe ta kama su da laifuka biyar da suka hada da hadin baki da kuma yin sojan-gona.

Ma’aikatar Kudi da cigaban Tattalin Arziki ta jihar ce ta kama su duka su biyun da laifin fitar da shaidar biyan kudi da rasiti na bogi a matsayin shaidar biyan kudin Hajji na 2019 ga maniyyata.

Sannan kuma an kama su da laifin ƙin saka N73, 715,286.62 a asusun Hukumar Hajji ta Jihar Bauchi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button