Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Taki karbar shawara tana daukar hotuna da shafaffun mazaunan ta, martanin Datti Assalafiy ga Maryam Yahaya

Taki karbar shawara tana daukar hotuna da shafaffun mazaunan ta, martanin Datti Assalafiy ga Maryam Yahaya

Kamar yadda kuka sani dai bayan jarumar masana’antar kannywood Maryam Yahaya ta sami sauki daga rashin lafiyar data sha fama, sai kuma ta fara sakin sabbin hotunan ta tana wallafawa a shafin ta na sada zumumta instagram.

Advertising

Ganin haka ne yasa wasu daga cikin abokanan sana’ar ta suke bata shawara kan cewa ta daina wallafa hotunan ta sai ta gama warewa gaba daya, amma haka tayi kunnen uwar shegu da maganar da suka fada mata.

To a wannan ‘yan kwanakin ma dai sai muka ango wasu zafafan hotunan da Maryam Yahaya ta sake wallafawa a shafin ta na sada zumun ta instagram wansa ta dauka a Kasar Dunai Daular Larabawa.

Inda hotunan nata suka dauki hankulan masoyn fa har ma da wadan da suke bibiyar ta a shafin nata na instagram.

Advertising

To a yau kuma sai muka sami wata wallafa a daga shafin shahararran marubucin nan Datti Assalafiy, inda yake martani akan sabbin hotunan da jaruma Maryam Yahaya ta dauka a Kasar Dubai Daular Larabawa, inda yake cewa.

SHAMULOKI KENAN.

Jaruma Maryam Yahaya taki karban shawara
kan ta dena sakin hotuna a media, domin dole su Datti Assalafiy suyi sharhi tunda jarumace a Masana’antar Hausa fim masu koyar da tarbiyya a Kasar Hausa.

Ga jaruma Maryam nan a Kasar Dubai Daular
Larabawa tana sakin zafafan hotuna da wannan shafaffen mazaunan nata.

Kalar hannayenta yayi daban da kalar fuskanta, hoton data dauka a sahara k0 rigar mama babu, k0 wa take son burgewa a haka oho?.

Tsakani na da Allah ina matukar jin tausayin
yarinyar nan, Hausa film bai mata rana ba, da alama jaruma Maryam ta zabi hanyar duniya ta fada mata gaskiya ba mutane ba.

Allah Ya kyauta.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button