Advertising
Advertising
Labarai

Abin daya kamata Duniya ta sani game da zargin DCP Abba Kyari, Daga mai magana Datti Assalafiy

Abin daya kamata Duniya ta sani game da zargin DCP Abba Kyari, daga Datti Assalafiy

Shahararran marubucin nan Datti Assalafiy ya wallafa wani dogon rubutu a shafin sa na sada zumunta instagram tare da wata bidiyo, akan kama “DCP Abba Kyari” da aka yi inda ya fara da cewa.

Advertising

ABINDA YA KAMATA DUNIYA TA SANI
GAME DA ZARGIN DCP ABBA KYARI
.

Daga Datti Assalafy:

Wadannan mutane da zaku gani a cikin bidiyo sune masu safarar hodar iblis (cocaine) daga birnin Adis-ababa na Kasar Ethiopia zuwa Nigeria.

Advertising

Ga sunayensu kamar haka:

(1) Emeka Alphonsus Ezenwame dan
shekara 45.

(2) Chibunna Patrick Umeibe dan shekara
29.

Abinda ya faru shine Emeka da Chibunna sun dauko hodar |b|is daga Kasar Ethiopia, sai suka sauka a filin jirgin kasa da kasa na Akanu Ibiam International Airport Enugu Nigeria, jami’an hukumar NDLEA dake filin jirgin sun tantancesu suka barsu suka wuce da hodar iblis din.

To sai aka samu wani dan Ieken asiri (INFORMANT) ya Iabartawa dakarun IRT yaran DCP Abba Kyari sai suka bi diddigin mutanen suka kama su.

Wannan bidiyon dakarun IRT ne yaran Abba Kyari suka dauka Iokacin da suke jefa tambayoyi wa masu safaran hodar iblis din bayan sun kamasu, ga hodar iblis din a hannunsu suna jawabin abinda ya faru.

Wannan abin duka ya faru bayan an dakatar da Sarkin Yakin Nigeria DCP Abba Kyari daga aiki, Sarkin Yaki bai sansu ba, bai da wata alaka da su ba||e alaka na safaran miyagun kwayoyi kamar yadda NDLEA tayi zargi.

Abida ya shigo da Sarkin Yaki cikin wannan mummunan cin amana shine ya 20 taimako ne domin a biya INFORMANT hakkinsa na kudi bayan dakarun IRT sunyi transfer din case din zuwa hukuma NDLEA domin su fadada bincike, bidiyon da aka nuna DCP Abba Kyari yana bawa jami’in NDLEA kudi ba na cin hanci bane.

Kudi ne da za’a biya INFORMANT hakkinsa,
informer din yana nan da ransa, kuma kudin ma na aro ne daga gurin wani.

Dan canjin kudi, aminci ne ta sa Abba Kyari cikin wannan rigimar tsakanin sa da jami’in NDLEA wanda aka sakayeshi cikin bidiyon, sai aka juya aka ku||a masa mummunan cin amana don a ruguzashi DCP Abba Kyari da Informant yake aiki.

Bai taba daukarsu da wasa, a kowace kasa a duniya jami’an tsaro suna da tsarinsu na yadda suke aiki da INFORMANT, suna biyansu, hatta shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kawo tsarin WHISTLE BLOWER kan yadda za’a biya kudi kaso mai yawa ga duk wani INFORMER da ya tona asirin cin hanci da rashawa tare da alkawarin boye sirrinsa.

https://www.instagram.com/tv/CaKpFspoZ8e/?utm_medium=copy_link

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button