Advertising
Advertising
Labarai

Jami’an tsaro na Amotekun dake jigar Ondo sun kama wasu ‘yan cirani guda 63 bayan sun boye kan su a motar shanu

Jami'an tsaro na Amotekun dake jigar Ondo sun kama wasu 'yan cirani guda 63 bayan sun boye kan su a motar shanu

Kai tsaye daga shafin shahararran marubuci Datti Assalafiy, kan labarin wasu mutane sittin da uku 63 da aka kama a jihar Ondo.

Advertising

Mai magana Datti Assalafiy ya wallafa labarin a shafin sa na sada zumunta kamar haka.

Jami’an hukumar tsaro ta Amotekun reshen Jihar Ondo, ta kama wata babbar mota a karamar hukumar Akure ta Arewa, dauke da maza kimanin 63 daga Arewacin Nijeriya.

Baya ga mutanen, an kuma dora wa motar shanu da raguna da babura, yayin da mutanen su ka boye cikin dabbobin da baburan kamar yadda rahotan AID Multimedia Hausa ta rawaito.

Advertising

Rahotanni sun ce, mutanen sun yi ikirarin sun taso daga Jihar Gombe, su na hanyar zuwa Legas kafln a taresu a kama su.

Direban motar mai suna Salisu Ahmed, yace su na kan hanyar su ta zuwa Legas ne, amma ya kasa yin bayani dangane da matasan da ke makale a motar.

Babban kwamandan Amotekun na jihar Ondo Cif Adetunji Adeleye, ya ce an kama mutanen ne, yayin da aka bincika motar aka gano ba dabobbi kadai da baburai da dauko ba, an cakudasu da mutane 63 da babura 1O masu rajista da sunan Yarbawa, da wasu 15 marasa rajista da kuma shanu 240.

Daman ba wannan ne karo na farko ba da ake
muzgunawa Hausawa ba, yayin da suke zuwa ci-rani a kudancin Kasar Najeriya, idan mukai nazari da duba da yadda ‘yan kudancin kasar basu samun muzgunawa ko cin mutunci idan suka zo ci-rani a Arewacin kasar.

https://www.instagram.com/p/CaICmwpo28F/?utm_medium=copy_link

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button