Advertising
Advertising
Labarai

‘Yan ta’adda sun bankawa wani kauye wuta tare da kashewa al’ummar kauyen da konewa dukiyoyin su

'Yan ta'adda sun bankawa wani kauye wuta tare da kashewa al'ummar kauyen da konewa dukiyoyin su

Wasu ‘yan ta’adda sun kone wani gari mai suna Turgar Zarumai inda suka bankawa kauyen wuta a jiya Asabar, dukiyar al’ummar kauyen tare da abincin su da sauran abubuwan amfani sun kone gaba daya, wanda gaba daya ‘yan kauyen sun gudu domin su tsira da ran su.

Advertising

Har yanzu dai al’ummar kauyen suna cikin firgici da fargaba a karamar hukumar mulki dake shanga, wanda ake ganin cewa matukar jami’an tsaro basu kai dauki ba to tabbas ‘yan ta’addan zasu kara kaiwa wani mummunan harin.

Har yanzu dai talakawan Arewa na wasu yankunan suna shan azaba kan ta’addancin dake addabar su, bayan haka akwai ire-iren Tungar Zarumai da ‘yan ta’ddan suka hallaka su wanda sun fi dubu tare da sace wasu domin neman kudin fan sa.

Inda ake hasashen nan gaba kadan Nigeria gaba dayan ta zata iya komawa kamar kasar mexico a baya, tabbas idan kuwa wannan hasashen ya tabbata to tabbas masu mulki sunyi bankwana da runtsa idanun su da sunan barci.

Advertising

Irin wannan kisan gillar da ‘yan ta’adda suke yiwa al’ummar wasu yankunan a Nageriya abin Allah wadai ne.

Ga hotunan yadda suka kowa kauyen.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button