Allah Sarki: Ali Jita tare da Fati Nigar sun tuna da tsohuwar soyayyar su wacce suka yi a baya
Allah Sarki: Ali Jita tare da Fati Nigar sun tuna da tsohuwar soyayyar su wacce suka yi a baya
Kamar yadda kuka sani dai Ali Isah wanda aka fi ssni da Ali Jita ficaccan mawakine a masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood, wanda ya jima yana rera wakokin soyayya.
Idan bazaku manta ba tsawon lokuta da suka shede Ali Jita tare da mawakiya Fati Nigar sun rera wata waka tare mai taken “Dawo Fatima Dawo”, wanda wakar tayi tasiri sosai a zukatan mutane musammam ma wanda suke tsaka da soyayya a lokacin.
To a yau ne kuma muka sami wata bidiyo daga tashar “Tsakar Gida” dake kan manhajar Youtube, inda suka wallafa bidiyo Ali Jita tare da mawakiya Fati Nigar inda suke tunawa da tsohuwar wakar da suka rera tare.
A cikin bidiyon zakuga yadda Ali Jita yake daukar Fati Nigar a da kuma shi kan sa inda suke wakar tare suna marmarin wakar domin ta shiga zukatan su.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin ganin yadda suke kewar wakar da suka rera tare mai taken “Dawo Fatima Dawo”.
Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.